30 Maris 2020 - 07:13
Mali : Ana Zaben ‘Yan Majalisar Dokoki Duk Da Barazanar Corona

A Mali an gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki yau Lahadi, bayan dage zaben sau da dama a cen baya.

(ABNA24.com) An gudanar da zaben duk da matsalolin da kasar ke fama dasu da suka hada da na tsaro da barazanar coronavirus da kuma sace madugun ‘yan adawa na kasar.

A karshen shekara 2018 ne wa’adin ‘yan majalisar dokokin kasar ya kawo karshe, amma aka yi ta tsawaita shi saboda tabarbarewar al’amuran tsaro da rikicin siyasa a kasar.

Duk da yanayin da ake ciki, gwamnatin kasar Mali ta yanke shawarar gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar, inda ta bukaci masu kada kuri'a da su tabbatar sun kiyaye da matakan kaucewa kamuwa da cutar COVID-19.

Gwamnatin Mali ta ce, kada kuri'a 'yancin 'yan kasa ne, kare kai da kare sauran jama'a daga cutar COVID-19 hakki ne a kan kowa.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya ayyana dokar ta-baci a fannin lafiyar kasar.




/129